Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta ce ta kama mutane 218 da ta ke zargi da safarar miyagun kwayoyi masu nauyin kilo 5,610 a Kaduna.
Kwamandan Hukumar NDLEA a Jihar Kaduna, Mista Ibrahim Braji ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a ranar Lahadi a Kaduna.
Braji ya ce wadanda ake zargin sun hada da maza 206 da mata 12, inda ya kara da cewa adadin mutanen ya hada da masu safara da masu ta’ammuli da miyagun kwayoyin.
Kwamandan ya ce, miyagun kwayoyin da aka cafke masu nauyin kilo 5,610 sun hada da Cannabis Sativa, Heroin, Cocaine, Methamphetamine, Tramadol da sauran magungunan da aka amince ayi mu’amala da su kadai a Asibitin masu tabin hankali.
Ya ce kamen da aka yi tsakanin watan Janairu zuwa Maris na wannan shekara, wani bangare ne na kokarin da rundunar ta ke yi na dakile amfani da ta’ammuli da miyagun kwayoyin.