Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun kama mamallakin Otal din Adekaz, Alhaji Ademola Afolabi Kazeem da ke jihar Legas, bisa laifukan da suka hada da safarar miyagun kwayoyi da kuma badakalar kudade.
Hakan na zuwa ne kwanaki 10 bayan da hukumar ta ayyana shi a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bisa zarginsa da hannu wajen safarar miyagun kwayoyi.
Idan dai za a iya tunawa a ranar Talata 1 ga watan Nuwamba ne hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta bayyana neman wanda ake tuhumar ruwa a jallo sakamakon rashin amsa gayyatar da aka yi masa da kuma umarnin da wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta bayar.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce: “An gano mutumin da ake nema ruwa a jallo, wanda ke daukar nauyin wasu masu safarar miyagun kwayoyi da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kama a yunkurinsu na fitar da hodar iblis a baya-bayan nan zuwa Dubai da UAE da sauran kasashe.
“A ranar Alhamis 10 ga watan Nuwamba, sakamakon matsin bincike, anyi nasarar cafke Adekaz wanda a halin yanzu yana tsare yana amsa tambayoyi.”