Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Katsina ta samu nasarar damke wadanda ake zargi da ta’ammuli da miyagun kwayoyi akalla mutum 345 a fadin jiha watan Janairu zuwa watan Mayun wannan shekara.
Kwamandan hukumar, Muhammad Bashir Ibrahim ya sanar da haka a wajan bikin ranar yaki da shan miyagun kwayoyi ta duniya na bana wanda aka kwashe mako daya ana gudanarwa. Ya ce akalla an saita wa mutane masu ta’ammuli da miyagun kwayoyi tunanisu kimanin 388 a wannan dan tsakanin.
Haka kuma NDLEA a Jihar Katsina ta shirya wani taron kara wa juna sani na wuni daya kan rawar da jami’ai za su taka wajen yaki da fataucin miyagun kwayoyi na hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro. Taron kara wa juna sanin ya gudana ne a shalkwatan hukumar da ke Katsina.