Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama wanda ya kafa kuma yake kula da cocin ‘The Turn of Mercy’, Adefolusho Olasele, wanda aka fi sani da Abbas Ajakaiye, bisa zarginsa da hannu wajen safarar miyagun kwayoyi da dama daga Ghana zuwa Nijeriya.
Fasto Olasele, wanda ya shafe watanni ba a san inda yake ba, an kama shi ne a ranar Lahadi, 3 ga watan Agusta, 2025, a cocinsa da ke Okun Ajah, yankin Lekki, a Legas.
- NDLEA Ta Cafke Masu Baburan Da Ke Kai Saƙon Muggan Ƙwayoyi A Abuja
- Dole Ne Afrika Ta Mayar Da Hankali Wajen Amfana Da Damarmakin Da Ke Tekunanta – Ɗantsoho
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi, ta ce, jami’an hukumar sun jira har zuwa lokacin da ya gama wa’azi na ranar Lahadi kafin su kama shi a lokacin da ya fito daga harabar cocin.
A cewarsa, faston ya gudu zuwa Ghana a cikin watan Yuni don gujewa kama shi bayan da jami’an tsaro suka alakanta shi da laifin safarar miyagun kwayoyi kulli biyu kimanin kilo 200 da aka gano a bakin tekun Okun Ajah a ranar 4 ga watan Yuni da kuma kilo 700 da aka samu a cikin motarsa ta kai sako a ranar 6 ga watan Yuli.