Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) reshen jihar Adamawa, ta kame haramtattun kwayoyi kimanin kilo 1845 tare da tsare mutum 365, ta kuma hukunta wasu mutanen 174, bisa samunsu da laifin sha da safarar miyagun kwayoyi a shekarar 2023 a jihar.
Mista Femi Agboalu, shugaban hukumar a jihar, ya sanar da haka a wani taron manema labarai a Yola, ya ce a tsawon lokacin hukumar ta kama kilo 1,081.9, na tabar wiwi (Indiya herm), ganguna 7 na formalin da aka fi sani da ( tsotsa ka mutu) da kilo 28.013, na maganin tari mai dauke da codeine.
- Sabon Dakin Binciken Da Aka Gyara Zai Inganta Aikin NDLEA — Marwa
- Tinubu Zai Kaddamar Da Kwamitin Gyaran Mafi Karancin Albashi Ranar Talata
Da yake ci gaba da bayyana nasarorin da hukumar ta samu cikin shekara guda a jihar shugaban ya ce “a shekarar an samu raguwar mutanen da aka kama da kashi 25 cikin 100 da kuma karuwar masu kama da kashi 33 cikin dari.
“Mun gode wa Allah da babu wani jami’inmu da ya rasa ransa a cikin shekaru ukun da suka gabata, duk da rundunar na fuskantar rashin isassun kayan yaki da masu safarar miyagun kwayoyi, saboda sauki babban nauyin da ya rataya a wuyanmu, tare da bude ofisoshi a kananan hukumomin jihar 21” inji Femi.
Haka kuma shugaban ya godewa shugaban hukumar NDLEA ta kasa Janar Buba Marwa (Mai murabus), da gwamnan jihar Ahamdu Umaru Finitri, bisa goyon bayan da suke baiwa rundunar, ya ce da ba domin gudumuwarsu ba, da hukumar bata kaiga cimma nasarorin da ta samu ba.
Sauran kayayyakin da rundunar ta kwato a cikin shekara da ta gabata sun hada da motoci uku da babur guda daya, da kuma kudi naira dubu dari takwas da ashirin da daya da dari biyu da saba’in (N 821,270,000), ya ce an tura kudin ga asusun gwamnatin tarayya.