Hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), reshen Jihar Kano, ta kama kwalaben Akuskura 8,000, wani hadin ganyayyaki da ake zargin yana dauke da haramtattun abubuwa da kuma wasu miyagun kwayoyi 48 (Cannabis satiba).
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Sadik Muhammad Maigatari ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata.
Maigatari ya kara da cewa, an cafke wani mutum mai suna Ali Muhammad, dan shekara 37 da haihuwa da laifin satar kayan da aka kama a hanyar Zariya zuwa Kano, Gadar Tamburawa.
“Al’amarin ya faru ne kusa Gadar Tamburawa, titin Zariya zuwa Kano, a lokacin da wata motar tirela da ke jigilar kaya daga Legas zuwa Maiduguri.
“Tirelar cike take da Keke Napep a ciki, inda aka boye kayan laifin a tsakanin sassan Keke Napep din da kuma karkashin tirelar tare da gina kataren wani katako, domin kayan.”
“Jami’an yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), sun gano wadannan kayan laifuka ne, ta hanyar jajircewa da himma da kuma sanin makamar aiki.”
Rundunar ta ce, dukkannin abubuwan da aka baje kolin nasu da wadanda ake zargi da aikata laifin, na nan a hannun hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, inda ake ci gaba da bincike a dakin gwaje-gwaje, don tabbatar da kayan laifin da aka kama.
Hukumar ta NDLEA, ta bukaci jama’a su kasance cikin taka-tsan-tsan, tare da kai rahoton abubuwan da ake zarginsu da aikatawa ko kuma abubuwan da suka shafi muggan kwayoyi ga ofishinta ko wata hukuma mafi kusa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp