Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta kama wasu masu safarar haramtattun kwayoyi, ciki har da wani matashi mai shekaru 22 da ake zargin yana sayar da magungunan ga ‘yan bindiga a Jihar Kano.
A yayin wannan kamu, jami’an NDLEA sun dakatar da Muhammad Mohammed a kan hanyar Bichi-Kano tare da magunguna 277 na pentazocine a jikin sa. Haka kuma, an kama wani mutum mai suna Mohammed Abdulrahman Abdulaziz, mai shekaru 43, a Rimin Kebe, ƙaramar hukumar Ungoggo inda aka samu kilogiram 30 na skunk.
- Tsarin BRICS Ya Zama Muhimmin Dandalin Hadin Kai Na Kasashe Masu Tasowa
- NDLEA Ta Kama Wani Mutum Mai Shekaru 75 Da Laifin Safarar Muggan Kwayoyi
A cikin wani sumame kuma, NDLEA ta dakatar da kokarin fitar da hodar Iblis mai nauyin gram 500 wanda aka ɓoye cikin littattafai 20 na addini zuwa Saudiyya. Hakanan, jami’an NDLEA a Surulere, Legas, sun kama mota ɗauke da kilogiram 1,100 na skunk.
A Jihar Bayelsa, NDLEA ta kama kilogiram 557.2 na skunk da kilogiram 5.6 na methamphetamine, yayin da a Kebbi, aka yi ram da wata mota ɗauke da kilogiram 97 na skunk da aka ɓoye a cikin buhun gawayi.
A Jihar Edo, NDLEA ta kai hari a gonakin tsabar wiwi guda biyu a cikin dajin Egbeta na ƙaramar hukumar Ovia ta arewa maso gabas, inda aka lalata fiye da kilogiram 3,700 na shuka wiwi da kuma gano kilogiram 136.5 na wiwi da aka sarrafa.
Shugaban NDLEA, Brig.-Gen. Mohamed Buba Marwa, ya yaba wa jami’an hukumar bisa ƙoƙarinsu wajen yaki da magungunan da kwayoyi na haram, yana mai kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani abu da ke shafar safarar magunguna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp