Hukumar Yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) a Kano ta kama wani matashi mai suna Umar Adamu Umar, mai shekaru 27, bisa zargin safarar wiwi da darajarta ta haura Naira miliyan goma.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun hukumar a Kano, Sadiq Muhammad Maigatari, ya fitar ranar Asabar, an kama Umar ne daga ƙaramar hukumar Fagge, a ranar 6 ga watan Agusta, 2025, a kan hanyar Zariya zuwa Kano. An gano cewa yana ɗauke da kilogiram 9 na wiwi da aka ɓoye ɗauki 19.
- Rajistar Katin Zaɓe: Gwamnatin Kano Za Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kan Jama’a
- NDLEA Ta Kama Dilolin Ƙwaya 49 A Kano
Binciken NDLEA ya nuna cewa an kawo miyagun ƙwayoyin ne daga Legas zuwa Kano. Hukumar ta ce kayayyakin da aka kwace suna da darajar da ta kai sama da Naira miliyan goma, kuma wannan kame da haifar da babban cikas ga masu fataucin, domin ya katse musu hanyoyin samun kuɗi da kuma rabawa. Kakakin hukumar ya ce hakan zai taimaka wajen kare al’umma daga illolin zamantakewa da tattalin arziƙin da ke tattare da fataucin miyagun ƙwayoyi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp