Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun Kwayoyi ta kasa (NDLEA) reshen jihar Kano, ta samu nasarar kwace buhuhunan tabar Wiwi 116 da nauyinsu ya kai kilo 1,500.
Kwamandan Hukumar reshen jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad ne ya bayyana hakan a ranar Talata, inda ya ce, wannan kwacen, babbar nasara ce ga hukumar.
Ya ce, “jami’anmu sun shafe wata biyu suna bibiyar isowar haramtacciyar tabar wacce nauyinta ya kai kilo 1,500 tare da samun nasarar cafke mutum biyu da muke zargin sune masu kayan.
“An kwace kayan ne a garin Garindau kusa da Gadar Wudil da ke karamar hukumar Wudil a jihar Kano a ranar Larabar da ta gabata.
“An samu nasarar cafke kayan ne biyo bayan samun bayanan sirri, cewa, an yo fataucin haramtacciyar tabar wiwi daga Lokoja zuwa jihar Jigawa.
“Wadanda aka kama sune, Jonathan Nuhu dan shekara 45 wanda ya fito daga kauyen Kanke a jihar Filato da kuma Muhammad Abubakar, dan shekara 18 wanda ya fito daga karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano.”