Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, (NDLEA), Buba Marwa ya bayyana cewa hukumarsa ta kuduri aniyar fatattakar masu miyagun kwayoyi.
Marwa ya kara da cewa shaye-shayen miyagun kwayoyi da matasa ke yi abin tsoro ne, inda ya ce akwai alaka a bayyane tsakanin shaye-shayen miyagun kwarori da kuma karuwar aikata laufuka.
- Yadda Al’umma Za Su Taimaka Wa Makarantu
- Kotu Ta Daure Dillalan Miyagun Kwayoyi 15 Shekara 168 A Gidan Yari A 2023 – Marwa
Ya dai bayyana hakan ne a wurin kaddamar da littafi kan yaki da miyagun kwayoyi da ya gudana a Jihar Kwara.
Ya ce wannan littafin zai fadakar da matasa kan illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi, sannan kuma wadanda suke ciki tsamo-tsamo za su ga irin hatsarin da suke ciki.
Marwa ya bukaci gwamnati ta samar da fili da za a gina wa hukumar NDLEA bariki a dukkan fadin kasar nan. Ya kuma kira da a samar da isassun motocin aiki domin kara yaki da fatattakar ta’ammuli da miyagun kwayoyi.
A dai makon da ya gabata ne, Marwa ya bayyana cewa hukumar tana da ofisoshi a dukkan kananan hukumomi 774 da ke fadin Nijeriya a matsayin wani mataki na yaki da miyagun kwayoyi tun daga kasa har zuwa sama.
Tun da farko dai a nasa jawabin, shugaban kwamitin shirya kaddamar da littafin, Alhaji Mohammed Tunde Akanbi ya bayyana cewa an fassara wannan littafi a harshen Yarbanci domin fadakar da matasa illar ta’ammuli da miyagun kwayoyi tare da hanyoyin kare kai.