• English
  • Business News
Wednesday, October 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NDLEA Ta Kwace Kilo Giram 390 Na Muggan Kwayoyi

by Rabi'u Ali Indabawa
2 years ago
NDLEA

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi Ta Kasa sun kama wata babbar mota dake dauke tabar wiwi da ta kai kilogiram 76.9 na kasar Canada, wani nau’in tabar wiwi, daga wasu motoci guda hudu da aka yi amfani da su a cikin wani akwati mai lamba MSDU6686346 daga kasar Kanada, a tashar Port Harcourt, Onne, Jihar Ribas.

An kama miyagun kwayoyin ne a tsakanin ranar 1 ga watan Yuni zuwa 2 ga watan Yuni a yayin wani binciken hadin gwiwa na jigilar kayayyaki da jami’an hukumar kwastam ta Nijeriya suka gabatar.

  • Masana Da Jami’an Kasashen Sin Da Tanzania Sun Sha Alwashin Inganta Hadin Gwiwa Tsakanin Kasashe Masu Tasowa
  • Muna Fama Da Targade Sai Ga Karaya – ‘Yan Nijeriya

Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

“Wannan (kamamen) ya biyo bayan bukatar yin gwajin kashi 100 na jigilar kaya ne sakamakon bayanan sirri da hukumar ta samu a baya kan wata kwantena,” in ji Babafemi.

Ya kuma kara da cewa jami’an tsaro sun kai farmaki dajin Iwe da ke Karamar Hukumar Owan ta Yamma a Jihar Edo, inda suka samu wani katafaren dakin ajiyar kaya, inda suka ajiye buhunan jumbo guda 231 na wannan sinadari mai nauyin kilogiram 3,003 da aka kona. .

LABARAI MASU NASABA

Jami’an Tsaro Sun Kwato Wayoyi 45 Daga Hannun Wata Kungiyar Barayi

‘Yansanda Sun Kama Mutum Hudu Da Ake Zargi Da Aikata Muggan Laifuka A Yobe

Ya kara da cewa, “Aikin da ya kunshi daruruwan jami’an NDLEA dauke da muggan makamai a safiyar ranar Talata, 30 ga watan Mayu, ya biyo bayan samun bayanan sirri da aka yi cewa wani sarkin da ake nema ruwa a jallo ya ajiye tan na haramtattun kayan laifi a cikin dajin da ke shirin raba wa sauran sassan kasar nan.

“A Jihar Kano, an kama wasu mutum biyu, Ma’aruf Rabi’u da Abubakar Mustapha a ranar 30 ga watan Mayu a kan hanyar Zariya zuwa Kano tare da bulogi 260 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 139.4, yayin da Auwal Ibrahim aka kama shi da kilo giram 38 na abu daya a washegari. Titin Kaduna-Abuja, a ranar ne aka kama wata mata mai suna Bilkisu Isiya mai shekaru 35 da haihuwa, a Birnin Yero, Kaduna, dauke da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 5.6.

“A Jihar Borno, an kama wasu mutane biyu Abubakar Usman (wanda aka fi sani da Alhaji Mai Kero) da Adamu Yusuf a kauyen Bargu da ke Karamar Hukumar Shani, a ranar 3 ga watan Yuni, dauke da 165 na skunk mai nauyin kilogiram 140.7.

An kama su ne tare da goyon bayan sojoji, a cikin wani yanayi na masu tada kayar baya.”

Haka kuma an kama wata mata da ake zargin mai suna Hauwa Ibrahim ‘yar shekaru 25 a kauyensu dauke da kilogiram 6.4 na sinadari na tabin hankali, yayin da wani wanda ake zargi mai suna Alhaji Abubakar mai shekaru 27, kuma aka kama shi a shingen bincike na Njimtilo dauke da ampoules 4,200 na allurar pentazocine da nau’in D5 daban-daban, da kuma edol-5.

“An kama wani matashi mai shekaru 30 mai suna Iroko Wasiu a wani rukunin magunguna da ke Sabo Aba-Owolowo a kan titin Oyo-Ogbomoso a ranar 30 ga Mayu, kuma an samu kilogiram 31.2 na tabar wiwi a hannunsa, yayin da mutum biyu – Deji Adelabu, mai shekaru35.

Babafemi ya kara da cewa, an kama su da Mutiu Salau mai shekaru 37 a washegari a unguwar Sabo da ke kan titin Oyo-Ogbomoso da kuma yankin Awuro Dada a cikin Karamar Hukumar Orire ta Jihar Oyo tare da kwato tabar wiwi mai nauyin kilogiram 8 a hannunsu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jami’an Tsaro Sun Kwato Wayoyi 45 Daga Hannun Wata Kungiyar Barayi
Kotu Da Ɗansanda

Jami’an Tsaro Sun Kwato Wayoyi 45 Daga Hannun Wata Kungiyar Barayi

October 4, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Hudu Da Ake Zargi Da Aikata Muggan Laifuka A Yobe

October 4, 2025
Yaki Da Miyagun Kwayoyi: Kamfanin LEADERSHIP Da NDLEA Sun Kulla Kawance
Kotu Da Ɗansanda

NDLEA Ta Farmaki Masu Safarar Muggan Kwayoyi A Sassan Nijeriya

September 27, 2025
Next Post
Tinubu Na Fatan Na Zo Mu Yi Gwamnatin Haɗaka —Kwankwaso

Tinubu Na Fatan Na Zo Mu Yi Gwamnatin Haɗaka —Kwankwaso

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Rikon Kwarya: Shirin DSS Ne Na Damke Atiku Da Peter Obi Kafin Rantsar Da Tinubu

DSS Ta Kama Wani Matashi Da Ya Yi Kira A Yi Juyin Mulki A Kafofin Sada Zumunta

October 29, 2025
An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

October 29, 2025
Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra

Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra

October 29, 2025
ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC

October 29, 2025
‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa

‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa

October 29, 2025
Sanusi Ga ‘Yan Nijeriya: Ku Dora Wa Buhari Alhakin Matsatsin Tattalin Arziki Ba Tinubu Ba

Tsoron Boko Haram Ne Ya Sa Jonathan Ya Fasa Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II

October 29, 2025
Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

October 28, 2025
JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

October 28, 2025
An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

October 28, 2025
Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

October 28, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.