Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), Birgediya-Janar Mohammed Buba-Marwa (rtd), ya ce hukumar ta kama tan 9 na haramtattun kwayoyi da kudinsu ya kai Naira biliyan 1.5 sannan kuma ta kama mutane 1,078 a jihar Kano a shekarar 2022.
Ya ce, NDLEA ta kuma gano tare da lalata gonakin da ake noman tabar wiwi guda shida a kananan hukumomi biyar na jihar.
A cewarsa, an dauki isassun matakan da suka dace wajen jawo hankalin shugabannin jam’iyyun siyasa don sanin illar shaye-shayen miyagun kwayoyi a yayin da babban zaben 2023 ke gabatowa da kuma a rayuwar matasa ta yau da kullum.
Marwa ya ce, wasu ‘yan siyasa marasa kishin kasa na amfani da matasa a matsayin ‘yan daba a lokacin yakin neman zabe.
“ ‘yan siyasar na bai wa matasa kwayoyi domin su kawo rudani da lalata akwatunan zabe da haddasa sauran laifuka, musamman idan suka ji cewa za su iya faduwa zabe,” inji shi.
Shugaban hukumar ta NDLEA ya yi kira ga iyaye da masu kula da matasan da su wayar da kan jama’a game da yadda ‘yan siyasa marasa kishin kasa ke amfani da ‘ya’yansu gabanin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe.