Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta kwace kilogiram 150 na magungunan cutar tabin hankali daga hannun dillalan Magunguna a jihar Gombe.
Kwamandan hukumar ta jihar, Silvia Egwunwoke ce ta bayyana hakan a jiya yayin da take zantawa da manema labarai kan kamen.
Ta ce jami’an hukumar ta NDLEA a ranar 1 ga Satumba, 2022, yayin da suke aiki kan rahoton sirri, sun bi diddigin wata mota dauke da kwayoyi daga Onitsha zuwa jihar Gombe.
A cewarta, bayan gano magungunan, jami’an hukumar sun bi diddigin masu safarar Magungunan wanda hakan ya kai ga cafke wasu mutane shida da ake zargin suna da hannu wajen shigo da miyagun kwayoyi cikin jihar.
Silvia ta nemi iyaye da ‘yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki da su hada kai da hukumar wajen yakar shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar musamman a lokacin babban zaben 2023.