Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta cafke wani da take nema ruwa a jallo, Wasiu Sanni Gbolahan, wanda aka fi sani da (Teacher).
Gbolahan mai shekaru 64, dillalin gidaje ne, yana da ‘ya’ya bakwai da mata hudu, wanda daya daga cikinsu ta rasu.
Hukumar ta NDLEA ta kuma kama wani dattijo mai shekaru 56 mai suna Lawal Lateef Oyenuga, wanda ke shirin kai gram 400 na hodar iblis da aka boye a cikin takalmin sandals zuwa Jeddah ta kasar Saudiyya.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya ce jami’an NDLEA da ke kula da wurin tantance kayayyaki a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, a ranar Alhamis, 24 ga watan Nuwamba, sun kama Oyenuga da wani bakin takalmin sandals acikin kayanshi zuwa Jeddah ta kasar Saudiyya a jirgin Adis Ababa na Ethiopian Airways.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp