Jam’iyyar APC ta ce ta yi wa dan majalisar dattawa kuma tsohon mai tsawatarwa na majalisar, Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume afuwa, kan yadda ya fito fili ya soki salon jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu da jam’iyya mai mulki kan kunci da tsadar rayuwa da ake fuskanta a fadin Nijeriya.
Sakamakon wannan sukar, aka tsige Ndume daga mukaminsa na babban mai tsawatarwa a majalisar dattawa saboda jajircewarsa na fadin gaskiya ga masu mulki a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin kwanan nan.
- Ɓata-gari Sun Cinna Wa Sakatariyar APC Wuta Tare Da Lalata Kadarorin Gwamnati A Jigawa
- Sin Ta Yi Kira Ga ICC Da Ta Martaba Ikon Shari’a Na Sudan
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Majalisar Dattawa a zamanta na ranar 17 ga watan Yuli ta sauke Ndume a matsayin mai tsawatarwa sannan ta maye gurbinsa da Sanata Mohammed Tahir Monguno (Borno ta arewa).
Amma da yake jawabi ga manema labarai bayan taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC na kasa (NWC) tare da Sanata Ndume a Abuja ranar Talata, Ganduje ya ce, bangaren gudanarwar jam’iyyar zai rubutawa majalisar dattawa cewa, NWC ya yi wa Ndume afuwa.