• English
  • Business News
Wednesday, October 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ndume Ya Gargaɗi Tinubu Kan 2027: “An Taɓa Yi Wa Jonathan Irin Wannan”

by Abubakar Sulaiman
5 months ago
Ndume

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume, ya bayyana cewa bai goyi bayan yunƙurin wasu gwamnoni na jam’iyyar APC na mara wa Shugaba Bola Tinubu baya don sake tsayawa takara a 2027 ba. Ya bayyana hakan ne a shirin ‘Sunday Politics’ na Channels TV, inda ya ce yanayi bai dace da hakan ba yanzu.

Sanatan ya tuna cewa a 2015 tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya samu goyon bayan gwamnoni 22 na jam’iyyar PDP, amma hakan bai hana shi faɗuwa a hannun Muhammadu Buhari na APC ba. Ya ce irin wannan goyon baya daga gwamnoni ba ya tabbata da nasara.

A ranar 22 ga Mayu, 2025, gwamnoni 22 na jam’iyyar APC sun amince da Tinubu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar don zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Amma Ndume ya bayyana cewa bai goyi bayan wannan mataki ba saboda matsin rayuwa da rashin tsaro da ke addabar ƙasar.

Ya ce lokacin da aka fara jefa ƙuri’ar amincewa da Tinubu a wani taro a Banquet Hall na Villa, ya fice daga wajen. Ya bayyana cewa ba dalilin zuwansa taron ba ne, kuma ficewarsa ba yana nufin ya fice daga APC ba, sai dai ya ce bai dace a yi hakan ba a yanzu.

Ndume ya ce tarihi ya nuna cewa irin wannan taron mara baya ba ya nufin nasara. Ya kawo misalin Jonathan wanda duk da samun goyon bayan gwamnoni 22 a 2015, ya sha kaye. Ya ce “yan siyasa na sauya jam’iyya amma masu kaɗa ƙuri’a ba sa sauya ra’ayinsu,” yana mai bayyana cewa ba a ɗaukar darasi daga tarihi.

LABARAI MASU NASABA

Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci

Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci
Manyan Labarai

Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci

October 29, 2025
ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa
Manyan Labarai

Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC

October 29, 2025
‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa
Manyan Labarai

‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa

October 29, 2025
Next Post
He Lifeng Zai Ziyarci Birtaniya Tare Da Halartar Taron Farko Na Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Amurka 

He Lifeng Zai Ziyarci Birtaniya Tare Da Halartar Taron Farko Na Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Amurka 

LABARAI MASU NASABA

COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

October 29, 2025
Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

October 29, 2025
Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci

Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci

October 29, 2025
Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

October 29, 2025
Gwamnatin Rikon Kwarya: Shirin DSS Ne Na Damke Atiku Da Peter Obi Kafin Rantsar Da Tinubu

DSS Ta Kama Wani Matashi Da Ya Yi Kira A Yi Juyin Mulki A Kafofin Sada Zumunta

October 29, 2025
An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

October 29, 2025
Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra

Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra

October 29, 2025
ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC

October 29, 2025
‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa

‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa

October 29, 2025
Sanusi Ga ‘Yan Nijeriya: Ku Dora Wa Buhari Alhakin Matsatsin Tattalin Arziki Ba Tinubu Ba

Tsoron Boko Haram Ne Ya Sa Jonathan Ya Fasa Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II

October 29, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.