Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare ta Ƙasa (NECO), ta fitar da sakamakon jarrabawar 2025.
Kashi 60.26 daga cikin 100 na ɗaliban da suka zauna jarrabawar sun ci aƙalla darusa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi.
- Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
- Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi
Shugaban NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ne, ya sanar da haka a Minna, babban birnin Jihar Neja.
Ya ce ɗaliban da suka samu nasara sun kai 818,492.
Ya ƙara da cewa, idan aka cire darusan Turanci da Lissafi, adadin ɗaliban da suka ci aƙalla darusa biyar ya kai 1,144,496, wanda yake kashi 84.26 cikin 100.
A cewarsa, ɗalibai 1,367,210 ne suka yi rajistar jarrabawar; maza 685,514 da mata 681,696.
Daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka rubuta jarrabawar, waɗanda suka haɗa da maza 680,292 da mata 678,047.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp