Gwamnatin jihar Neja, ta ce tana shirin tafiya kotu idan har gwamnatin tarayya ta ki ba ta kaso 13 na kudaden da ake samu daga tashoshin samar da wutar lantarki da ke jihar.
Gwamnan jjhar Nejan Umar Muhammed Bago, ya ce al’ummar jihar Neja na shan bakar wahala a kusan duk shekara ba tare da samun wata kulawa ba duk da gudunmuwar da kasarsu ke bayarwa.
- Za Mu Karfafa Yaki Da Miyagun Kwayoyi A Jihar Zamfara – Gwamna LawalÂ
- Fashewar Tankar Gas Ce Sanadin Tashin Gobara A Ofishin Jakadancin Canada – FEMA
Alhaji Ibrahim Bolagi sakataren labaran Gwamnan Neja, ya ce yanzu idonsu ya bude dole su nema wa mutanensu hakkinsu.
Wannan dai wata alama ce da ke nuna jihar Neja na son bin sahun jihohin da ke samar da albarkatun mai a kudancin Nijeriya, da ke samun tagomashi na musamman daga gwamnatin kasar nan.
Gwamnatin jihar Neja ta ce daga filinta ne aka samar da Abuja, amma kuma babu wani amfani da ta ke samu daga wannan, sannan ga tashoshin samar da wutar lantarki guda hudu da suka hada da Shiroro, Jebba, da Kainji, yanzu kuma ga na Zungeru ana dab da kammalawa.
Masanin kundin tsarin mulkin Najeriya lauya Mainasara Kogo Umar ya ce duk Gwamnan na da damar bin hakkinsu, amma kamata ya yi Gwamnonin da abin ya shafa su hada kai.
Jihar Neja dai jiha ce da ke taimaka wa matuka gaya wajen samar da hasken wutar lantarki a Nijeriya duba da manyan tashoshin samar da wutar na jihar.