Gwamnatin Jihar Neja ta sha alwashin gyara makarantun rugagen Fulani domin inganta ilimin ‘ya’yan makiyaya.
Kwamishinan ma’aikatar kula da harkokin manoma da makiyaya na Jihar Neja, Hon. Umar Ahmed Rebe ne ya bayyana hakan a wani rangadin gani da ido a wasu rugagen Fulani da ya fara ziyarta a yankunan kananan hukumomin Bida da Katcha.
- Daukaka Karar Shari’o’in Zabe: Wasu Hukunce-hukunce Sun Yi Ba-zata
- Yawan ‘Yan Nijeriya Ya Doshi Miliyan 223 – Shugaban NPC
Kwamishinan ya ce ya kawo ziyara a sabuwar matsugunnin makiyaya a gundumar Kateregi da ke karamar hukumar Katcha, domin ganin irin matsaloli da suke fuskanta ta fuskar ilimi da ruwan sha.
Ya ce zai tabbatar gwamnatin jiha ta duba wannan yanayin, musamman a wannan makarantar da ya ga yara sama da dari suna karatu a karkashin bishiya.
Kwamishinan ya ziyarci wata makarantar rugar Fulani da ke Tudun Fulani a yankin Bida, ina ya tarar da dalibai masu karancin shekaru sama da dari da iyayen suke kula da su a makarantun sama da hamsin.