Yau Talata, Super Eagles za su fafata da Bafana-Bafana na Afirka Ta Kudu a garin Bloemfontein, wasan zagaye na 8 na neman gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya a rukuni na C.
Wannan wasa na da matuƙar muhimmanci ga Nijeriya wadda take matsayi na uku a rukuni, domin tana buƙatar nasara don ci gaba da fatan zuwa gasar a baɗi.
- Nan Gaba TIinubu A Wajen Opay Da Moniepoint Zai Nemi Rancen Kuɗi – Dino Melaye
- El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙara Kan Zargin Ƴansanda Da Cin Zarafinsa A Kaduna
A yanzu haka, Afirka Ta Kudu na gaba da Nijeriya da maki shida.
Sai dai akwai batun zabtare mata maki saboda zargin saka Teboho Mokoena a wasa duk da yana da jan kati sau biyu.
Idan hakan ta tabbata, tazarar maki tsakanin ƙasashen biyu na iya raguwa daga shida zuwa uku.
Idan Afirka Ta Kudu ta yi nasara yau, za ta tabbatar da zuwa gasar Kofin Duniya da za a buga a Arewacin Amurka a 2026, kuma karo na farko tun bayan 2010 lokacin da ta ɗauki nauyin gasar.
Nijeriya kuwa, wadda ta halarci gasar sau shida a baya, tana ƙoƙarin dawo da martabarta.
Nasarar da ta samu a kan Rwanda a wasan da ya gabata ta farfaɗo da ƙwarin guiwar masoyanta, duk da cewa a wasanni bakwai da ta buga na neman gurbin shiga 2026, sau biyu kacal ta ci.
Wasan na yau shi ne karo na 17 da ƙasashen biyu za su haɗu.
Nijeriya ta fi samun nasara sau takwas, inda aka tashi canjaras sau bakwai, sai Afirka Ta Kudu da ta yi nasara sau 2 kacal.
Ana jiran a ga ko Bafana-Bafana za su ƙara daurewa, ko kuma Super Eagles za su ƙwato matsayinsu a cikin manyan ƙasashen ƙwallon ƙafa na duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp