Yayin da wasu jarumai a masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood da sauran masana’antun shirya fina-finan da ke fadin duniya ke cewa; aikinsu na Fadakarwa, Nishadantarwa da kuma Ilimantarwa ne, jaruma Khadija Muhammad, wadda ta fito a manya-manyan fina-finan Hausa da suka hada da Gidan Sarauta, ta bayyana cewa; babu wani abu mai alaka da Fadakarwa, idan aka tambaye ta abin da ta zo yi a masana’antar mai dimbin tarihi.
“Babu wani abin da ya kawo ni masana’antar Kannywood, face neman kudi, duk da cewa; tun a lokacin kuruciya nake fatan zama ‘yar fim, hakan bai sa na dauki fim a matsayin wata hanya ta isar da sako don Fadakarwa ba, abin da na sani shi ne; ana samun kudi a Kannywood, kuma ni ma su na zo nema” in ji ta.
- Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
- Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
Da jarumar ke amsa tambaya a kan wace irin matsala ta fuskanta a yayin fara saka kafa cikin masana’antar, Khadija wadda ta ce mahaifiyarta Bafulatana ce ta bayyana cewa, babu wata wahala da ta sha yayin shiga masana’antar.
Ta ce, “Dole ne akwai kalubale da dama, wanda daga cikinmu muke fuskanta a yayin shigowa wannan masana’anta, amma dai ni babu wani abu da zan iya tunawa, illa wani wanda na iske a masana’antar ya karbi zunzurutun kudi har Naira 50,000 a mabanbantan lokuta da sunan zai yi min rijista a masana’antar, kuma bai yi ba, daga karshe ma na gano cewa; kudin rijistar duka-duka Naira 5,000 ne.
A wata hira da Khadija ta yi da gidan Rediyon Hikima, ta bayyana cewa, matukar ta samu abin da ya kawo ta masana’antar (Kudi), to nan da shekara daya ma; za ta iya shiga daga ciki, ma’ana za ta samu miji ta yi aurenta na Sunna.
Khadija, wadda ta ce; ita haifaffiyar birnin Maiduguri ce ta Jihar Borno, wadda zama ya dawo da ita birnin Kanon Dabo, ta kuma bukaci masu kallon su da su dinga nuna musu soyayya kamar yadda suke nuna wa sauran jaruman duniya, musamman wadanda ke cikin masana’antar Bollywood ta Kasar Indiya.
“Akwai bukatar dukkaninmu, mu hada karfi da karfe don ganin mun taimaki junanmu, ba mu koma gefe muna zagin junanmu ba, abin da ya sa na fadi haka kuwa shi ne, akwai lokacin da wani ya zo neman aurena, amma wasu suka zagaya baya suka hure masa kunne a kan cewa; kada ya sake ya aure ni, saboda ni jarumar fim ce. Ta kara da cewa; mu ma Hausawa ne kamar mafi yawan masu kallonmu, sannan kuma bai kamata ku yi la’akari da duk wani abu da kuka gani a cikin fim, wajen yanke hukuncin cewa, halin dan fim kenan ko a zahiri ba.
Daga karshe, Khdadija ta ce; “Dukkanninmu ‘yan fim, muna kokari wajen ganin mun killace kanmu( Sirrinta al’amuranmu), domin kauce wa zargi, duk wani wanda ka ga yana fallasa halayensa na zahiri a shafukansa na sada zumunta, to ba dan fim ba ne, kawai yana zuwa neman taimako wajen masu shirya fina-finai ne su saka shi ya fito sau biyu ko sau uku a fim, domin su samu na cefane, amma ba lallai ne ya zama cikakaken dan fim ba.