“Abin alfahari ne gare ni kasancewar na zama mace ta farko dake iya tuka jirgin kasa. Kamfanin Sin ya kyautata rayuwata”. Issa Fatima Abiola wadda ta sanyawa kan ta sunan “Baiyang” a Sinanci, ta bayyana hakan yayin da na zanta da ita a shekarar 2021. Ita ce mace mai tuka jirgin kasa ta farko a Najeriya, bayan kamfanin Sin ya horas da ita, matakin da ya kyautata rayuwarta matuka.
A halin yanzu, Issa Fatima Abiola, tana iya tuka jirgin kasa bayan horon da kamfanin Sin ya ba ta.
- Kakakin Ma’aiktar Tsaron Sin Ya Gabatar Da Yadda Aka Gudanar Da Atisayen Hadin Gwiwa Na Sojojin Sin Da Tanzaniya Da Mozambique
- Sin Da Afirka Aminai Ne Wajen Neman Zamanantar Da Kansu
A daya bangaren kuma, masu aikin jiyya da Sin da Comoros suka yi hadin gwiwa wajen horar da su, suna ceton rayukan mutane da dama daga cutar zazzabin cizon sauro. Kana matasan Tanzaniya da suka yi karatu a Sin suna kokarin yada fasahohin noma na zamani a kasarsu. A gare su nesa ta zo kusa a rayuwar su, karkashin hadin gwiwar Sin da Afrika a fannin daga karfin samun bunkasuwa bisa dogaro da kansu.
Sinawa kan cewa “Guntun gatarinka ya fi sari ka ba ni”, saboda haka a ganinsu abu mafi muhimmanci shi ne taimakawa kasashe masu tasowa ciki har da kasashen Afirka, da karfin samun bunkasuwa ta hanyar dogaro da kai. Hakan ya sa kasar Sin gabatar da shirin hadin gwiwa da Afrika kan wasu manyan ayyuka 9, ciki har da aikin nan na daga karfin samun ci gaba, a gun taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika da aka gudanar a watan Nuwamban shekarar 2021.
Hadin gwiwar Sin da Afrika, wajen daga karfin samun bunkasuwa ta hanyar dogaro da kai, na dora muhimmanci sosai kan ainihin bukatun Afirka, lamarin da ya cika burin jama’a, kuma yake bunkasa hadin gwiwarsu don samun ci gaban Afrika mai inganci. (Mai zane da rubutu: MINA)