A halin yanzu za mu iya cewa nesa ta zo kusa game da kera jirgin kasa mafi gudu a duniya da kasar Sin ta kuduri aniyar kammalawa a shekarar nan ta 2025. Yanzu haka an kammala kera jirgin samfurin CR450, kuma har ya fara zirga-zirgar gwaji a layin dogo na jirgi mai matukar gudu daga Shanghai zuwa Chongqing zuwa Chengdu domin tantancewa.
Daga cikin ka’idojin da ake son jirgin ya cika kafin a fara jigilar fasinjoji da shi, ana bukatar ya yi zirga-zirgar da ta kai adadin kilomita 600,000 ba tare da tangarda ba, inda tuni ya yi gwajin tafiyar kilomita 450 cikin sa’a guda, har ma ya kure maneji zuwa gudun kilomita 896 cikin sa’a daya.
Jigrin kasa na CR450 wanda aka kaddamar da muhimmin shirin samar da shi a shekarar 2021, an rage masa nauyi da kashi 10 cikin dari a kan na baya mai gudun kilomita 350 cikin sa’a daya domin inganta tattalinsa. Haka nan, an sake wa giyarsa fasali da inganta burkinsa domin rigakafin makalewar kafafunsa a kan layin dogo.
Bugu da kari, an yi wa tsarin cikin jirgin wani irin kayataccen shiri ta yadda aka rarraba shi sashe-sashe. Bangaren zaman hamshakai ya kunshi kujerun da za a iya daidaita su zuwa mazaunin taro ta yadda mutane za su fuskanci juna.
A bangaren kananan kujeru kuwa, an tsara kujerun ta yadda mutum zai yi walwala, kana aka samar da wurin makala cajin waya da kananan tebura da mutum zai iya ajiye wayarsa ya yi kallon bidiyo da ita. Haka nan, ana iya rage hasken lantarki daidai da yadda ake bukata bisa aunawa da hasken waje.
Tun daga lokacin da kasar Sin ta fara kera jiragen kasa masu saurin gudu a shekarar 2007 da samfurin CRH1 mai gudun kilomita 250 cikin sa’a guda, ba ta tsaya ba har zuwa yanzu da ta kera wannan sabon na zamani samfurin CR450 wanda shi ma an yi masa tsarin da za a ci gaba da inganta shi.
Wannan fasaha wacce ta kara jaddada matsayin kasar Sin na ci gaba da zama jagora a fagen kere-keren jirgin kasa mafi gudu a duniya, ba kasar Sin kawai za ta amfanar ba har ma da sauran sassan duniya musamman a wannan zamani da kasar ta Sin ke kara bude kofarta ga kasashen waje da kuma neman cimma burin samar da al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)