Newcastle ta lallasa Leicester da ci 3-0 a ranar Litinin a gasar Firimiya Lig ta Kasar Ingila, wasan wanda ya kasance na 8 a jere da Leicester City ta buga ba tareda jefa kwallo a raga ba, Newcastle da Eddie Howe ke jagoranta na fatan ganin sun samu gurbi a gasar Zakarun Turai na badi, tun da farko dai sun lashe gasar League Cup a watan da ya gabata.
Yanzu haka su na matsayi na biyar a kan teburin Firimiya, inda suke da maki daya da Chelsea da ta ke matsayi na hudu, Leicester City kuma a nata bangaren ka iya komawa gasar ‘yan dagaji ta Championship idan aka doke su a wasansu na gaba a gasar.
- Yadda Tashar Jirgen Ruwan Apapa-Moniya Za Ta Taimaka Wa Masu Safarar Fitar Da Kaya
- NIMASA Za Ta Adana Wa Nijeriya Dala Biliyan 400 A Shekara Daga Cazar Kudaden Safarar Kaya
Newcastle, wacce arzikinta ya bunkasa tun bayan da mamallakanta ‘yan Kasar Saudiyya su ka karbi iko a shekarar 2021, ta na neman sake samun damar buga gasar Zakarun Turai tun bayan wanda aka kore ta a shekarar 2023/24 bayan shafe shekaru ashirin.
Howe, wanda ya jagoranci Newcastle lashe babban kofi na farko cikin shekaru 56 a wasan da su ka doke Liverpool a Wembley a watan da ya gabata, ya na da damar kara haskakawa a wannan kakar wasanni ta bana mai dimbin tarihi a wajen Newcastle.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp