Dan wasan Brazil, Neymar ya zama dan wasa na hudu a yawan ci wa Paris St-Germain kwallaye a tarihi bayan da a ranar Asabar PSG ta doke Brest 1-0 a wasan mako na bakwai a gasar Ligue 1 ta Faransa.
Neymar mai shekara 30 ne ya ci kwallon kuma kwallo ta 110 kenan, ya haura matakin tsohon dan wasan tawagar Portugal, Pauleta a yawan ci wa PSG kwallaye kuma Lionel Messi ne ya bai wa Neymar kwallon da ya zura a raga ta takwas a kakar nan a wasa na bakwai a babbar gasar ta Faransa.
Tsohon dan wasa Edison Cabani ne kan gaba a yawan ci wa PSG kwallaye a tarihi, sai Zlatan Ibrahimobic na biyu mai sannan Kylian Mbappe na uku, sai kuma yanzu da Neymar shima ya shiga layi.
Sai dai ana tsaka da wasa aka bai wa dan wasan Brest, Christophe Herelle jan kati, sakamakon ketar da ya yi wa Neymar daga baya aka soke, bayan da na’urar BAR ta fayyace cewar dan wasan PSG ya yi satar gida kafin ketar da aka yi masa.