Hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) da hukumar kwallon kafa ta Nijeriya (NFF), sun kaddamar da wani karamin filin wasa wanda aka kashe dala miliyan 1.19 domin tallafa wa ci gaban kwallon kafa a Jihar Kebbi.
Tsohon gwamnan jihar, Atiku Bagudu, ya aza harsashin aikin da aka gina a kan titin Kalgo a cikin Birnin Kebbi a watan Satumba.
- Jami’ar Ambrose Alli Ta Lashe Lambar Yabon Fasaha Ta Nijeriya
- CITAD Ta Horar Da Matasa 40 Kan Fasaha A Kano
Yayin kaddamar da filin wasan a ranar Juma’a, gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya jaddada shirinsa na goyon bayan matasa ta kowane fanni.
Ya ce gwamnatinsa na duba yiwuwar dawo da gasar wasannin motsa jiki na shekara-shekara kuma za ta ci gaba da tallafa wa kungiyoyin wasanni a jahar.
Gwamna Idris wanda ya samu wakilcin Alhaji Safiyanu Garba-Bena, shugaban ma’aikatan gidan gwamnati ya godewa shugaban hukumar NFF, Ibrahim Gusau, da kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta jihar Abubakar Chika-Ladan, bisa kokarinsu.
Gwamnan ya yi kira ga kungiyar kwallon kafa ta jihar da NFF da su mayar da jihar ta zama cibiyar kula da kwallon kafa ta kasa, domin bunkasa hazikan ‘yan kwallon kafa da ke jihar. Ce
Idris ya kara da bada tabbacin a shirye gwamnatin sa ta ke na taimakawa tare da hadin gwiwa wajen bunkasa harkar kwallon kafa da duk wasu wasanni a jihar.