Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta miƙa ta’aziyyarta game da rasuwar mahaifin gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo, Alhaji Ahmed Momohsani Ododo, wanda ya rasu a ranar 19 ga watan Agusta, 2025, yana da shekara 83.
A cikin saƙon ta’aziyyar da shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta bayyana marigayi Alhaji Momohsani a matsayin shugaba na gari, uba, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’ummarsa hidima.
- Kura Za Ta Ce Da Kare Maye
- Nijeriya Ta Kori Ƙarin ‘Yan Ƙasashen Waje 51 Da Aka Ɗaure Bisa Laifin Ta’addanci Da Zamba A Intanet
Ƙungiyar ta ce za a yi kewar jagorancinsa da jajircewarsa wajen tabbatar da zaman lafiya.
Ta ƙara da cewa ya yi rayuwa mai albarka, ya bar tarihi na aiki tuƙuru da gaskiya.
NGF ta lura cewa wannan rashi ba na iyalan Gwamna Ododo kaɗai ba ne, har da al’ummar Jihar Kogi baki ɗaya, waɗanda suka amfana da hikimarsa.
Ƙungiyar ta yi addu’ar Allah Ya bai wa iyalan marigayin haƙuri da juriya, sannan ya gafarta masa Ya kuma yi masa rahama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp