Babbar direktar kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana a wata hira ta musamman da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua a kwanakin baya cewa, a matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban-daban.
Ngozi Okonjo-Iweala ta ce, a koda yaushe kasar Sin ta kasance mai goyon bayan tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban. A matsayinta na muhimmiyar kasa a fannin tattalin arziki a duniya, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a tsarin ciniki cikin ‘yanci de bude kofa. Ta kara da cewa, za a gudanar da taron ministoci karo na 13 na kungiyar WTO a watan Febrairun shekarar badi, don haka, tana fatan taron zai gudana cikin nasara, don haka ana bukatar dukkan membobin WTO ciki har da kasar Sin su yi kokari tare.
Ngozi Okonjo-Iweala ta yi imanin cewa, manufofin tattalin arzikin kasar Sin ba wai kawai za su iya kara kuzari a cikin gida ba, har ma za su taimaka wajen farfado da kasuwancin duniya. Kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a tsarin cinikayya na duniya, kuma yadda kasar take gudanar da harkokin kasuwanci mai yakini, zai taimaka wajen inganta bunkasuwar tattalin arziki da cinikayyar sauran kasashe da yankuna, musamman ma kasashe masu tasowa. (Zainab)