Gwamnatin sojin Nijar ta bude rajista domin tattarawa tare da adana sunayen wadanda ake zargi a kasar da harkokin ta’addanci, kamar yadda tashar talabijin na kasar RTN Tele Sahel ya ruwaito a jiya.
A wata doka da shugaban sojin kasar Birgediya Janar Abdourahmane Tiani ya sanya wa hannu, ta ce duk wani mutum da ya shiga rajistar, za a kwace kadarorinsa, a hana shi tafiya, sannan za a iya kwace shaidar zama dan kasar Nijar.
- Turkiyya Da Nijar Na Tattauna Ƙulla Kawancen Soji Da Tattalin Arziki
- Wainar Da Aka Toya A Taron ‘Yan Jarida Na Hausa A Nijar
Za a sanya mutum ne idan yana taimakon ta’addanci ko dai shiga ciki ko tsarawa ko kasancewa cikin kungiyar ta’addanci ko aware ko wata kungiya da ke barazana ga zaman lafiyar kasar.
Laifukan da za a duba sun kunshi daukar makami domin yaki da kasar, bayar da bayanan sirri ga kasashen waje, taimakon kasashen waje shigowa kasar da kuma fitar da wasu bayanai ko kalamai da za su iya tayar da zaune tsaye a kasar.
Tun bayan hambarar da Mohamed Bazoum daga mulki ne kasar take fuskantar karuwar harkokin ta’addanci, inda aka fi kai hare-hare a kan sojin kasar, musamman a yankin Tillaberi.
A wani labarin kuma, Rahotanni na cewa akalla sojojin Nijar bakwai ne ake zargin ‘yan bindiga sun kashe a ranar 26 ga watan Agusta bayan wani hari da ake kyautata zaton mayakan al-Kaeda ne suka kai a yankin Tillaberi mai fama da rikici a yammacin Nijar.
Shafin tsaro na taswirorin Afirka ta Yamma ya wallafa a shafinsa na D cewa karin sojoji 10 sun bace bayan faruwar lamarin.
Harin dai ya faru ne da misalin karfe shida na safe agogon kasar, inda wasu da dama daga cikin mayakan kungiyar Katiba Hanifa masu alaka da Jama’at Nasr al-Islam wal Muslimin (JNIM) suka kewaye tare da kai farmaki kan wani sansani na rundunar tsaron Nijar (GNN) a Bouloundjounga da ke Tillaberi.
Wannan wurin yana da kusan kilomita hudu daga Samira mai nisan kilomita 10 daga kan iyaka da Burkina Faso.
A martanin da aka mayar, an gudanar da aikin share fage a yankin, kuma an tura wani jirgi mara matuki domin hana ‘yan bindigar tsallaka kogin Sirba.
Sansanin Bouloundjounga, wanda ke da sojoji kusan 80 na da alhakin kare mahakar zinari da ke kusa da tsaunin Samira.