Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya ce duk da cewa Nijeriya kasa ce mai ɗimbin jama’a da ƙabilu mabanbanta, amma ba ƙasa ce mai wuyar jagoranta ba.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wajen buɗe cibiyar Bakhita ICT a sakatariyar Katolika da ke jihar Sokoto, inda ya jaddada cewa, ƙarfin Nijeriya ya ta’allaƙa ne kan haɗin kan ta duk da cewa, tana da ɓangarori daban-daban.
- Ma’aikatan Jinya Sun Yaba Wa Gwamnatin Kaduna Kan Aiwatar Da Sabon Tsarin Albashi
- Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang
“Akwai abubuwa masu kyau da yawa a Nijeriya, saboda hadin kanmu a cikin bambance-bambancenmu, kuma wannan ne ya kai Nijeriya wannan darajar da take a yau saboda bambance-bambancenta.
“Idan aka yi amfani da bambance-bambancen tare da kyakkyawan shugabanci da haɗa kai, to za a mutunta mu (Nijeriya) kuma a sanya mu cikin manyan kasashe a duniya,” in ji shi.
Tsohon shugaban ya kara da cewa gaskiya da rikon amana a bangaren shugabanni na da matukar muhimmanci wajen tafiyar da kasar.