Sufeto Janar na ‘yansanda na kasa, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewar rundunar ‘yansandan Nijeriya ba ta shirya kirkiro ‘yansandan jihohi ba.Â
Sufeton ya bayyana hakan ne yayin wani taro a Abuja, wanda IGP Egbetokun, ya wakilce shi, inda ya ce Nujeriya ba ta shirya amfani da ‘yansandan jihohi ba.
- Sojoji Sun Lalata Masana’antar Sarrafa Burodin ‘Yan Ta’adda A Borno
- Tsaro: Nijeriya Za Ta Karbo Jiragen Yaki 24 Daga Kasar Italiya
Sufeton ‘yansandan ya bayyana cewa kirkirar ‘yansandan jihohi zai haifar da rikicin kabilanci, wanda hakan zai haifar wa Nijeriya karin matsaloli.
A cewarsa kirkiro ‘yansandan jihohi zai kuma kai ga kafa wasu rundunoni da dama a fadin Nijeriya, wanda a cewarsa ba su ne abin da kasar ke bukata a yanzu ba.
Ya ja hankali kan cewa akwai yiyuwar gwamnonin jihohi su yi amfani da ‘yansandan wajen cimma wasu muradansu na siyasa maimakon barin su, su yi aikin da ya dace a dokance.
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, Abdulsalami Abubakar da wasu manyan ‘yan siyasa na daga cikin wadanda suka halarci taron a Abuja.
Idan ba a manta ba a baya baya-bayan nan gwamnatocin jihohi sun matsa lamba kan bukatar gwamnatin tarayya ta samar da ‘yansandan jihohi domin rage yawaitar ayyukan ta’addanci.