A rahoton da wata kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Global Petrol Price’ ta fitar, ta bayyana cewa, a halin yanzu Nijeriya ne kasa ta 6 a Afrika a arhar mai a fadin nahiyar Afirka kuma ita ce na 22 a fadin duniya a kididdigar da aka yi zuwa ranar 1 ga watan Janairu 2024.
Kasashen Iran da Libya, wadanda dukkan su mambobi ne na kungiyar masu hakar man fetur na duniya (OPEC), sune a kan gaba a matsayin na daya na da biyu a kasashen da ake sayar da man fetur mafi arha a duniya.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, matsakacin farashin man fetur a duniya shi ne Dala $1.30 wato Naira 1,200 a kan lita daya.
- Cire Tallafin Fetur: Gwamnatin Katsina Ta Amince Da Raba Hatsi Da Takin Zamani Don Tallafawa
- Radadin Cire Tallafin Man Fetur: Kwan-gaba Kwan-baya Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar Kwadago
Amma kuma a Nijeriya ana sayar da man fetur din ne a kan Dala 0.722 (naira 660.25) a daidai ranar 8 ga watan Janairu 2024.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, yayin da farashin man fetur a kasuwannin duniya yake daya amma kasashe daban-daban na samar da tallafi ne ga al’ummar su don rage musu radadin tsadar man fetur din, haka ya sa ake samun bambanci na farashin mai a tsakanin kasashen duniya.