‘Yan wasan kwallon Super Eagles na Nijeriya za su buga wasan sada zumunci da kasar Guinea a Abu Dhabi ranar Litinin, kamar yadda Daraktan Sadarwa na Hukumar NFF, Ademola Olajire ya bayyana.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya a ranar Asabar a Abuja, ya ruwaito cewa wasan sada zumuncin na daga cikin shirye-shiryen da Super Eagles ke yi gabanin gasar cin kofin Afrika karo na 34 a Cote d’Ivoire.
Kocin na Super Eagles, José Peseiro, yana son ya gane yanayin wasan ‘yan kwallonsa yayin da ake tunkarar gasar.
Wasan sada zumuntar zai zo kwanaki bakwai kacal kafin Super Eagles wadda ta lashe gasar sau uku ta buga da Equatorial Guinea a filin wasa na Alassane Ouattara da ke birnin Abidjan.