A karshen mako ne Hukumar Kwastam ta Nijeriya da takwarar ta na Jamhoriyyar Benin suka dauki alkawarin aiki tare domin samar da sabbin hanyoyin inganta harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.
A sanarwa da jami’in watsa labarai na hukumar, Abdullahi Maiwada, ya sanya wa hannu aka kuyma raba wa manema labarai a Abuja, ya bayyana cewa, hadin gwiwar zai kuma tabbatar da an aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a taron da aka yi a tsakanin hukumomin a Kwatano kwanakin baya.
- Bangaren Amurka Ya Mayar Wa Bangaren Sin Da Kayayyakin Tarihi 38 Da Suka Bata Daga Sin
- Sharhi: Kokarin Fahimtar Yanayin Tattalin Arzikin Sin Ta Bangarorin Ayyuka Guda 3
Ya kuma ce ziyarar za ta kara karfafa dangatatakar da ke tsakanin hukumomin, wadda ta kasance na shekara da shekaru ne.
“Muna sane da yarjejeniyar da aka kulla a tsakanin shugabannin kasashen biyu, Shugaba Patrice Talon na Jamhoriyyar Benin da kuma shugaba Bola Tinubu na Nijeriya, domin samar da ci gaban tattalin arzikin kasashen.”
Da yake maraba da tawagar hukumar kwastam ta Nijeriya, Shugaban Kwastam na Jamhoriyyar Benin, Adidjatou Hassan Zanoubi, ta jadda aniyarta na aiwatar da dukkan yarjejniyar da aka cimma a tsakanikn kasashen biyu.
Ta kuma kara da cewa, wannan yarjejeniyar da suka cimma a tsakanin su yana nuna irin yadda kasashen biyu suka dauki shirin bunkasa tattalin arzikin kasashen su da matukar muhimmanci.