Shekaru shida bayan yarjejeniyar musayar takardun kudade ta kasa da kasa, da aka kulllan Babban Bankin Kasar China da Bakin Alumma na kasar China, sun sake sabunta yarjejeniyar da Babban Bankin Nijeriya CBN.
Gundarin kudin yarjejeniyar, ta kai Naira tiriliyan 3.28 ko kuma Naira biliyan 15, na kudin kasar China wato yuan, wacce ta kai kwatankwacin dala biliyan 2.09.
- Gwamnan Kano Ya Yi Sabbin NaÉ—e-NaÉ—e
- Dokar Haraji Za Ta Ƙara Jefa Al’umma Cikin Talauci – Gwamnatin Kano
A cikin wata sanarwa da Babban Bankin na kasar China ya wallafa a shafinsa na Internet, wa’adin yarjejeniyar za ta kai ta shekaru uku, wacce kuma za a iya sake sabunta yarjejeniyar idan bukatar hakan taso.
Sanarwa ta kara da cewa, sake sabunta wannan yarjejiniyar za ta kara karfafa hada-hadar hadaka a tsakanin China da Nijeriya, tare da kuma kara fadada yin amfani da takardun kudaden kasashen biyu da kara bunkasa hada-hadar kawunaci da kuma zuba hannun jari.
Kazalika, sabunta yarjejeniyar za ta taimakawa kasashen biyu, wajen rage dogaro a kan takardar dalar Amurka don gudanar da hada-hadar kasuwanci.
Tun farko dai, an kulla wannan yarjejeniyar ce, a watan Afirilun 2018 wacca kuma take da wa’adi na shekara uku, duba da yadda ake fuskantar karancin dalar Amurka a kasar nan.
Bugu da kari, jarjejeniyar za ta kara fadada yin amfani da tardun kudi na kasashen biyu tare da kuma kara karfafa hada-hadar kudade,
Nijeriya dai, ta kasance babba wajen yin hadaka, domin kasar ta China, na shigo da danyen mai, iskar Gas wanda daga baya, inda su kuma suke shigo da sauran kaya da bana da ba, ciki har da ababen hawa da na’urorin kayan wutar lantarki daga kasar ta China.
A 2023, Nijeriya ta shigo da kayan daga kasar China, da kudinsu ya kai na dala biliyan 11.2, inda kuma kayan da aka fitar daga kasar zuwa Asiya, kudinsu ya kai dala biliyan 2.4.
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bayyana cewa, a 2023 yawan hada-hadar kasuwancin d aka yi a tsakanin Nieroya da kasar China, ta kai ta yawan dala biliyan 22.6.
Kashim
Kashim ya bayyana haka ne, a cikin watan Numbar 2024, a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a yayin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga kasar China.
Mataimakin kwamitin dindin na kungiyar kasar China NPCÂ Mista Zhang Kingwei ne, ya jagoranci tawagar a lokacin ziyarar.
Shettima ya kara da cewa, huddar jakadanci da ke a tsakanin Nijeriya da China, na kara fadada a duk shekara zuwa kashi 33.
Tabbasa Nijeriya ta kasance, babbar kawar kasar China wajen yin hadaka, musamman wajen zuba hannun jari a fannonin bunkasa tatttalin arzkin Nijeriya.
Misali, dangantar kasuwanci a tsakanin kasashen biyu ta kwanan baya, an mayar da hankali ne, wajen aikin samar da makamashi ga Nijeriya.