Kungiyar Mercy Corps ta kasa da kasa, ta koka a kan yadda rikice-rikicen manoma da makiyaya a kasar nan ke yawan afkuwa.
Daraktan wannan kungiya ta ‘Mercy Corps’ a Nijeriya, Ndubisi Anyanwu ne ya sanar da hakan; a hirarsa da menema labarai a Jihar Kaduna, jim kadan bayan kammala wani taron masu ruwa da tsaki da kungiyar ta gudanar a jihar.
- Za A Bude Shafin Karbar Bashin Dalibai A Ranar 24 Ga Mayu
- Shugabannin Sin Da Rasha Sun Tattauna Da Juna
Ya ce, kungiyar ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki ne a karkashin tallafin USAID.
Anyanwu ya kara nanata cewa, wannan rikici na manoma da makiyaya na jawo wa Nijeriya tabka asarar kimanin Naira biliyan 4.8 a duk shekara.
A cewarsa, kungiyar ta kiyasta asara ta akalla kimanin dala miliyan 12 da ake yi a duk shekara, sakamakon wannan rikici na manoma da makiyaya.
Daraktan ya ci gaba da cewa, daukar matakan gaggawa kan wannan rikici da ke faruwa a tsakaninsu; shi ne kadai babbar mafita ga zaman lafiyar wannan kasa.
Anyanwu ya ce, mahalarta taron sun tattauna a kan matsalolin da ke kawo rikicin tare da aiwatar da abubuwan da za su kawo zaman lafiya cikin gaggawa.