Tawagar Super Eagles ta Nijeriya a yau Alhamis za ta fafata da takwararta ta ƙasar Benin a wasan zagaye na biyar na wasannin neman gurbin buga gasar kofin ƙasashen Afrika da za a buga a ƙasar Moroco a shekarar 2025.
Nijeriya ta na matsayi na ɗaya da maki 10 yayinda ƙasar Benin ke bi mata a matsayi na 2 da maki 6, idan Nijeriya ta doke Benin a yau hakan zai ba ta damar buga gasar ƙasashen Afrika ta shekarar 2025 a Moroco.
- Super Eagles Ta Hauro Matsayi Na 36 A Jadawalin Duniya Na FIFA
- An Zargi FIFA Da Kin Biyan Hakkokin ‘Yan Wasa
A wasan farko da ƙasashen biyu su ka haɗu a Abuja, Nijeriya ce ta doke Benin da ci 3 da nema inda Victor Osimhen ya jefa ƙwallo ɗaya Ademola Lookman ya jefa kwallaye biyu a ragar Benin.