Daya daga cikin dattawa a masarautar Rano mai rike da sarautar Dan Kaden Rano, Alhaji Muhammadu Inuwa na II, ya bayyana cewa akwai bukata addu’a daga daukacin al’ummar Nijeriya, domin samun dauwamanman zaman lafiya, tsaro, da karuwar arziki a wannan kasar, musammamn a wannan lokaci da za a rantsar da sabbin shugabanni.
Dan Kaden Rano ya bayyana haka ne a ranar Laraba da gabata lokacin da yake zantawa da manema lab-arai a Jihar Kano.
- Yadda Manyan Jam’iyyu Suka Fada Cikin Rikici Bayan Zabe
- Dalilan Da Suka Sa Messi Ya Shiga Jerin Mutum 100 Masu Daraja A Duniya
Har ila yau, ya ce wannan lokaci na karshen watan Azumin Ramada na shekarar 1444 bayan hijira, lokaci ne na karba addu’ar al’umma, don haka akwai bukatar sadaukarwa da dagewa na nema wa Nijeriya wadataccen tsaro, wanda hakan zai kawo karshen wasu matsalolin da suka addabi kasar nan.
A cewarsa, akwai bukata ga daukacin al’ummar wannan kasa na bai wa shugabanni kyakkyawan hadin kai don samun nasarar mulikin da shugabancin na samun ci gaban Nijeriya.
A karshe Dan Kaden Rano, yaba wa mai martaba Sarkin Rano, Alhaji Kibiru Inuwa, kan kyakkyawan shugabanci da masarautar ke samun na kokarin hada kan al’umma da sauran abubuwan ci gaba da masarautar Rano ke yi na wayar da kan mutane.