Shugaban Majalisar wakilai, Rt Hon. Dakta Abbas Tajuddeen ya bayyana cewa Nijeriya ba za ta kai ga tudun mun tsira ba har sai an baiwa sarakunan gargajiya damar taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da lamuran kasa.Â
Abbas ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin majalisar sarakunan gargajiya ta kasa karkashin jagorancin Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar a ranar Litinin a ofishinsa da ke Abuja.
Ya ce akalla mambobin majalisar wakilai guda dari daga majalisa ta goma, suna da nasaba da sarautar gargajiya, don haka, majalisar wakilai za ta hada karfi da majalisar dattawa da kuma majalisun jihohi wajen ganin an baiwa sarakunan gargajiya dama a kundin tsarin mulkin kasar nan.
Tunda farko a jawabinsa, Shugaban Majalisar sarakunan gargajiya ta kasa, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar wanda Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar ya wakilta ya ce, manufar ziyarar tasu ita ce taya murna ga shugaban majalisar wakilai, Rt Hon Dr Tajuddeen Abbas a kan zabarsa da aka yi a matsayin shugaban majalisar wakilai ta goma.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya bukaci ganin sarakunan gargajiya sun samu matsayi a kundin tsarin mulkin kasa ba dan yin wata gasa da zababbun shugabanni ba, sai dai don samun damar ba da gudunmawa bisa doka wajen ciyar da kasa gaba.