Ƙungiyar Transparency Internaltional ta fitar da rahotonta na ayyukan cin hanci da rashawa a duniya cikin shekara ta 2024, wato Corruption Perception Inded.
Rahoton ya yi nazari ne kan ƙasashe 180 bisa la’akari da hujjojin masana da kuma ‘yan kasuwa kan matsalar rashawa na kowace kasa
- Thomas Bach Ya Bai Wa Cmg Izinin Sarrafa Watsa Labarun Gasar Olympics Ta Lokacin Hunturu Ta Milan Ta 2026
- Fatara Da Talauci Na Yi Wa ‘Yan Nijeriya Miliyan 13 Barazanar Fadawa Kangin Talauci A 2025 — Rahoto
Haka nan rahoton ya dogara da majiyoyi 13 masu zaman kansu domin dora kasashen kan mizani daga sifili zuwa 100; sifili na nufin matsalar rashawa ta yi muni sosai yayin da 100 ke nufin babu matsalar baki daya.
Rahoton ya kara fito da bambancin da ke tsakanin kasashen da ke bin tafarkin dimokuradiyya da kuma wadanda ke bin tsari na kama-karya.
Lamarin ya nuna cewa kasashen da ke bin tafarkin dimokuradiyya sau da kafa na da matsakaicin maki da ya kai 73, wadanda ke bin tsarin dimokuradiyya mai cike da kurakurai kuma na da matakaicin maki 47 sai kuma kasashen da ba su bin tafarkin dimokuradiyya wadanda ke da matsakaicin maki 33.
Ƙasashen da suke da saukin cin hanci a duniya
Mafi yawan kasashen da rahoton ya nuna cewa babu yawaitar matsalar cin hanci da rashawa suna a nahiyar Turai ne.
Bakwai daga cikin kasashen 10 na farko, wadanda ba su da matsalar Rasha duk a yankin Tarayyar ta Turai suke.
Qasar da ta fi kowace a duniya samun maki a bangaren yaki da rashawa ita ce Denmark, wadda take da maki 90.
Sai kuma Finland mai maki 88, ta uku kuma ita ce Singapore, wadda ke a kudu maso gabashin nahiyar Asiya.
Ga yadda kasashen 10 na farko suka kasance:
1. Denmark – Maki 90
2. Finland – Maki 88
3. Singapore – Maki 84.
4. New Zealand – Maki 83.
5. Ludembourg – Maki 81.
6. Norway – Maki 81.
7. Swtizerland – Maki 81
8. Sweden – Maki 80.-
9. Netherlands – Maki 78-
10. Austria – Maki 77.
Sai dai rahoton na Tranparency International ya ce duk da cewa kasashen Turai su ne suka fi samun yabo a rahoton, to amma makin da suke samu ya ragu cikin shekara biyu a jere.
Rahoton ya ce wasu shugabannin kasashen na Turai sun mayar da hankali wajen “abin da zai dadada wa harkar kasuwanci kawai a maimakon abubuwan da za su inganta rayuwar al’umma”.
Ƙasashen da ke kurar-baya
Rahoton ya nuna cewa akasarin kasashen da ke kasan jadawalin suna a nahiyar Afirka ne, inda nahiyar ke da kasashe shida cikin 10 da suka samu maki mafi karanci.
Sauran kasashen sun fito ne daga nahiyar Amurka ta kudu sai kuma Gabas ta takiya.
Sudan ta Kudu da Somaliya su ne kasashen da ke kasan tebur, inda Sudan ta Kudu ke da maki 8 kacal yayin da Somaliya ke da maki 9.
170. Sudan – Maki 15 –
172. Nicaragua – Maki 14-
173. Ekuatorial Guinea – Maki 13
173. Eritriya – Maki 13-
173. Libya – Maki 13-
173.Yemen – Maki 177. Syriya – Maki 12 –
178. Venezuela – Maki 10-
179. Somaliya – Maki 9-
180. Sudan ta Kudu – Maki 8
Rahoton ya ce nahiyar Afirka, kudu da hamadar sahara ce ta samu maki mafi karanci. Hakan ya faru ne sanadiyyar rikice-rikice masu alaka da sauyin yanayi wadanda ke tarnaki ga ci gaban yankin.
Sai dai rahoton ya ce bunkasar yaki da rashawa a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Amurka wani abu ne na farin ciki, sai dai wannan ne karo na farko da aka samu haka a cikin shekara 10, kuma ci gaban da maki daya ne kacal.
Mene ne matsayin Nijeriya da Nijar da Ghana?
A tsakanin Nijeriya da Nijar da Ghana, Ghana ce ta fi tabuka abin kirki, inda take a matsayi na 80 bayan samun maki 40.
Sai Jamhuriyar Nijar, wadda take a matsayi na 107 bayan samun maki 34.
Nijeriya na a matsayi na 140 inda ta samu maki 26, tare da wasu kasashen kamar Medico da Iraki da Kamaru.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp