Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa biyayyarsa a siyasa tana ga Nijeriya ne, ba ga kowanne mutum ko jam’iyya ba.
El-Rufai ya yi wannan bayani ne yayin ziyarar da ya kai Jihar Kano, inda ya gana da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, da kuma shugabannin jam’iyyar SDP na jihar.
- Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Ayyukan Sadarwa
- Akwai Ƙarin Gishiri A Yawan Masu Sauyin Jam’iyya Zuwa APC – El-Rufai
Ya ce dalilin da ya sa ya koma jam’iyyar SDP shi ne domin ya gina wata madaidaiciyar hanya ta siyasa da za ta ceto ƙasar nan.
“Shekaru goma sha biyu da suka wuce, mun kafa jam’iyyar APC kuma muka kayar da shugaban Æ™asa mai ci. Amma yau abubuwa sun canza. Muna haÉ—a kan ‘yan Nijeriya da suka gaji da halin da ake ciki a Æ™arÆ™ashin jam’iyyar SDP, wacce ke da adalci da dimokuraÉ—iyya,” in ji El-Rufai.
Ya kuma ƙara da cewa bai taɓa fifita jam’iyya sama da Nijeriya ba.
“Lokacin da abubuwa suka fara lalacewa a lokacin shugaba Buhari, na fito na faÉ—i gaskiya. Lokacin da tsarin sauya fasalin Naira ya jefa jama’a cikin wahala, na Æ™alubalanci gwamnati duk da cewa jam’iyyar APC ce ke kan mulki. Na fi biyayya ga Nijeriya fiye da kowane mutum,” in ji shi.
El-Rufai ya ƙaryata jita-jitar cewa fushinsa da gwamnatin Shugaba Tinubu ne ya sa ya fice daga APC.
Ya ce yana da shekaru 65, kuma babu wani abu da ya rage masa a siyasa da zai nema, sai dai kawai yana jin cewa matsalolin Nijeriya sun yi tsanani sosai wanda ba zai zauna ya yu shiru ba.
“Zan iya yin ritaya cikin kwanciyar hankali, amma Nijeriya na fuskantar babbar barazana. Wannan ba don kaina ba ne – don ceton Æ™asa ne,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa dole a zaɓi shugaban ƙasa mai nagarta da hangen nesa, ba wai kawai din ya fito daga wata jiha ba.
“Matsalolin da muke fuskanta sun fi girman la’akari da inda mutum ya fito. Muna buÆ™atar shugabanni masu hangen nesa da Æ™warewa don gyara Nijeriya,” ya bayyana.
Da yake magana kan sauya sheƙar wasu ‘yan siyasa zuwa APC, El-Rufai ya ce jam’iyyar SDP tana mayar da hankali ne kan gina goyon baya daga jama’a, ba wai kawai neman manyan ‘yan siyasa ba.
“Gwamna É—aya yana da Æ™uri’a É—aya ne kawai. Jama’a ne ke yin zaÉ“e, ba manyan ‘yan siyasa ba,” ya jaddada.
A ƙarshe, El-Rufai ya ce tafiyar SDP tana ci gaba da karɓuwa a dukkanin sassan Nijeriya, ba a yankuna kaɗan kaɗai ba.
“Muna ci gaba da gina goyon baya a faÉ—in Æ™asar nan. Aikin gina Æ™asa yana faruwa ne a tsakanin talakawa, ba kawai a kafafen yaÉ—a labarai ba,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp