Rundunar Sojin Nijeriya, ta aike da dakaru 177 zuwa kasar Guinea Bissau don taimakawa wajen wanzar da zaman lafiya a kasar.
Shugaban sashen gudanarwa na rundunar sojin kasa ta Nijeriya, Manjo Janar Boniface Sinjen ne, ya bayyana haka a ranar Laraba lokacin bikin yaye sabbin sojojin musamman na tallafa wa ayyukan ƙungiyar ECOWAS a cibiyar horas da sojoji ta Jaji da ke Jihar Kaduna.
- Ƴansanda Sun Kama Matar Da Ta Sheƙe Mijinta Har Lahira A Yobe
- Ana Ganawa Tsakanin ASUU Da Gwamnatin Tarayya
Yayin da yake jawabi ga dakarun kafin tafiyarsu zuwa Guinea-Bissau, Manjo Janar Sinjen, ya ce kasar na fama da matsalolin shugabanci, lamarin da ka iya haifar da barazana ga zaman lafiyar yankin Yammacin Afirka.
Ya kara da cewa aike dakarun zuwa Guinea-Bissau da gwamnatin ƙasar ta yi ta hanyar ECOWAS ya nuna irin goyon bayan ga Nijeriya ke bai wa Guinea-Bissau domin samun zaman lafiya
Ya ce za su yi kokarin agance matsalolin da kasar ta fuskanta da kuma ƙarfafa dimokuradiyyarta da kuma wanzar da zaman lafiyar kasar.
Nijeriya dai na zama jigo a lokutan wanzar da zaman lafiya a kasashen da ke yammacin Afrika.
A lokacin tsohon shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya nada tsohon shugaban kasa na babbar jami’yyar adawa ta PDP, Goodluck Jonathan a matsayin babban jakadan wanzar da zaman lafiya a Burkina Faso, bayan sojoji sun hambarar da gwamnatin dimokuradiyya a kasar.