Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa, Nijeriya ta gurfanar da masu daukar nauyi tare da tallafawa ta’addanci da kuɗaɗe fiye da 100 a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Tinubu, wanda sakataren gwamnatin tarayya (SGF), George Akume, ya wakilta, ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Talata a taron kungiyoyin yaki da masu daukar nauyin ta’addanci da kuma yaki da cin hanci da rashawa (AML/CFT/CPF) wanda Hukumar Leken Asiri ta Nijeriya (NFIU) ta shirya.
- Kasar Sin Ta Kara Sabbin Guraben Aikin Yi A Birane Miliyan 12.56 A Shekarar 2024
- Fashewar Tankar Mai A Suleja: An Kai Mutum 20 Manyan Asibitocin Abuja Don Samun Kulawa Ta Musamman
Ya ce, “mun samu ci gaba wajen tunkarar barazanar ta’addanci da sauran laifuffukan ta’addanci, ta hanyar gagarumin matakin da jami’an tsaronmu suka dauka. A bisa hikimarmu ta yaki da masu tallafawa ‘yan ta’adda, ta hanyar kokarin ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, mun gano tare da gurfanar da sama da 100 a cikin shekaru biyu da suka gabata.
“Ta hanyar datse hanyar samun kudade, kayan aiki, mun hana Boko Haram da ISWAP kai hare-haren ta’addanci a kan al’ummominmu da ‘yan kasa.”
Tinubu ya kara da cewa, tsarin datse hanyar samun kudaden daukar nauyin ta’addanci, ita ce hanya mafi aminci da duniya ta karba wajen yaki da ‘yan ta’adda.