A daren ranar 19 ga wata, agogon wurin, an watsa shirin fadakarwa na shagalin murnar bikin bazara na Babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin CMG na shekarar 2025 a hasumiyar Iconic dake cibiyar harkokin kasuwanci a sabuwar fadar mulkin kasar Masar. Kuma wannan shi ne shekara ta biyu da aka watsa shirin a cibiyar harkokin kasuwanci ta sabuwar fadar mulkin kasar Masar.
Hasumiyar Iconic da aka fi sani da hasumiya mafi tsawo cikin nahiyar Afirka tana da tsawon mita 385.8, kuma tana tsakiyar cibiyar harkokin kasuwanci ta sabuwar fadar mulkin kasar Masar. A daren wannan rana, an kuma kaddamar da bikin nuna filitu na Chang’an da ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Masar da gwamnatin birnin Xi’an na Sin suka shirya cikin hadin gwiwa a cibiyar. (Mai Fassara: Maryam Yang)