Makarantar Likitoci ta Liɓerpool (LSTM), da gidauniyar Wellbeing Foundation Africa (WBFA) da Kwalejin ‘National Postgraduate Medical College of Nigeria’ (NPMCN), sun horar da likitoci sama da 220 da masu ba da shawara 140 don inganta kulawar gaggawa ga mata masu juna biyu.
Masu ruwa da tsaki sun bayyana hakan a wani taron da aka yi don nuna Shirin Ma’aikatan Lafiya ta Duniya (GHWP) na tallafin Gidauniyar 130, wanda ya ƙarfafa aikin gaggawar kulawa da mata, da jarirai, da horar da dabarun tiyata ga likitoci a duk faɗin ƙasar.
- Nijeriya Na Asarar Tiriliyan 3.2 Sanadiyyar Watsi Da Noma A Gandun Daji
- Yadda Nijeriya Za Ta Ci Gajiyar Fara Yada Shirye-shiryenta Na Rediyo Da Sinanci
Wacce ya kafa kuma Shugabar Gidauniyar Wellbeing Foundation Africa (WBFA), uwargidan tsohon gwamnan Jihar Kwara, Misis Toyin Saraki, ta jaddada rawar da shirin ke takawa wajen magance matsalar rashin lafiyar mata masu juna biyu a Nijeriya:
“Mun tsaya a wani muhimmin lokaci na kula da lafiyar mata masu juna biyu da jarirai a Nijeriya. Ta hanyar samar da ƙwararrun likitocin mata masu juna biyu da haɗa dabarun ceton rai a cikin tsarin karatun ƙasa, muna magance ɗaya daga cikin matsaloli na jinkirin kulawa, ƙarancin ƙwararrun masu kiwon lafiya a lokacin haihuwa.
“A yau, muna bikin shigar da shi a cikin tsarin karatun likitanci na Nijeriya. Ƙalubale a yanzu shi ne ci gaba da samun waɗannan nasarori da kuma tabbatar da cewa kowane ma’aikacin lafiya da ke hulɗa da mata masu juna biyu ya samu wannan horo,” in ji ta.
Shugaban tsangayar Kula da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu A Kwalejin Likitanci Ta Ƙasa (NPMCN), Farfesa Ayodeji Oluwole, ya bayyana hanyoyin da shirin ke bi wajen aiwatar da aikin:
” Wannan horo ya samar wa likitocinmu da fasaha ta zamani, kuma a cikin shekaru biyar, muna sa ran raguwar mutuwar mata masu juna biyu.
“Babban abin da ake buƙata shi ne a rage yawan mace-macen mata masu ciki a Nijeriya da Afirka, mun horar da likitoci kusan 220 da masu ba da shawara 140 a duk yankuna shida na siyasa.
“A yanzu haka, likitocin suna samun horo a babban asibitin ƙasa dake Abuja; hakan na da matuƙar muhimmanci wajen cimma manufofin gwamnatin tarayya na kula da lafiyar mata masu juna biyu,” in ji shi.
Farfesa Sanusi Ibrahim na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri ya bayyana cewa a Arewacin Nijeriya, mace-macen mata masu juna biyu na da matuƙar tayar da hankali.
“Wannan shirin ya ƙarfafa wa likitoci da ma’aikata, da dabarun ceton rai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp