Cibiyar kula da hada maguna ta Nijeriya tare da hadin gwiwar hukumar kula da ilimin da fasaha sun bayar da horo kan fasahar hada maguna a kwalejojin fasaha da kimiyya da ke fadin Nijeriya.
Bayar da horon ya gudana ne a shalkwatan ma’aikatan ilimi, a wani yukuri na hada kan masu ruwa da tsaki kan fasahar hada maguna.
Karamin ministan ilimi, Dakta Tanko Sununu shi ya jagoranci taron bayar da horon,wanda ya samu halartar sakataren ma’aikatar ilimi da sauran daraktoci.
- Jihar Oyo Na Horar Da Malaman Gona Domin Samun Wadatar Abinci
- DSS Ta Ceto Mutane 7 Da Aka Sace A SakkwatoÂ
Dukkan bangarorin guda biyu wadanda suka dauki nauyin bayar da horon sun amince a bai wa daliban da ke karatun difiloma ne kadai. Sun yaba wa shugabannin ma’aikatar ilimi wajen kokarin karfafa musu gwiwa kan bayar da wannan horo na fasahar hada maguna.
Sun kara da cewa a cikin nasarorin da aka cimma sun yi daidai da manufofin wannan gwamnati ta Shugaban kasa, Bola Tinubu na kara inganta harkokin kiyon lafiya.