Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta buga kunnen doki da takwararta ta Afirika Ta Kudu da ci 1-1 a filin wasa na Toyota dake birnin Bloemfontein dake kasar Afirika Ta Kudu.
Kyaftin din Nijeriya Troost Ekong ne ya ci gida a minti na 25 da fara wasan kafin fan wasan bayan Nijeriya Calvin Bassey ya farke kwallon dab da za a tafi zuwa hutun rabin lokaci.
Wannan sakamakon ya sa Super Eagles din suka rasa tikitin kai tsaye da zai kaisu gasar Kofin Duniya, amma kuma sunada wata damar, idan sukayi kokarin karewa a mataki na biyu a rukunin C.
Zuwa yanzu kasashen Moroko da Tunisia ne kawai kasashen da suka samu nasarar zuwa gasar ta Duniya da za a buga a kasashen Amurka, Mexico da Canada.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp