Tawagar kwallon kafa Super Eagles dake wakiltar Nijeriya ta sake buga canjaras da kasar Zimbabwe a wasan neman gurbin buga kofin Duniya na shekarar 2026 a Amurka,Mexico da Canada.
A wasannin biyu da Nijeriya ta buga a rukunin C mai dauke da kasashen Afirika Ta Kudu, Lesotho, Zimbabwe,Rwanda da Benin,duka an tashi wasannin da ci 1-1.
A wasan na yau Musona ya fara ci wa kasar Zimbabwe kwallo a minti na 26 kafin Kelechi Iheanacho ya farke wa Nijeriya a minti na 67 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Talla