Ministan harkokin waje, Yusuf Maitama Tuggar, ya ce har yanzu ECOWAS a shirye ta ke domin tattauna da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar kan su saki Bazoum kafin a fara tattaunawar cire takunkumin da aka sanya wa Nijar.
Njeriya ta bukaci a saki hambararren shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum sannan kuma gwamnatin mulkin sojin kasar ta ba shi damar zuwa wata kasa, in ji ministan harkokin wajen Nijeriya.
- Kotu Ta Umarci Dawo Da Motoci 50 Da Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Kwashe
- Harin Jirgin Sojin Nijeriya Ya Haifar Da Rudani A Kaduna
A halin yanzu dai Nijeriya ce ke shugabantar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS), wacce ta kakaba wa Nijar takunkumi bayan juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Bazoum a watan Yuli.
ECOWAS dai ta yi ta kira a mayar da Bazoum kan karagar mulki ba tare da bata lokaci ba, amma gwamnatin sojin kasar ta ci gaba da tsare shi ta kuma ce tana bukatar shekaru uku kafin ta mayar da mulki ga farar hula.
“Muna bukatar su saki shugaba Bazoum domin a ba shi dama ya bar Nijar.
“Ba za a ci gaba da tsare shi ba. Zai je wata kasa da ta amince ta karbe shi. Daga nan za mu fara magana kan cire takunkumin da aka sanya wa kasar,” a cewar Tuggar.
Ya kuma ce har yanzu kungiyar ECOWAS a shirye ta ke don tattauna da gwamnatin sojin Nijar.
A ranar 10 ga watan Disamba ne shugabannin ECOWAS za su gana a Abuja, domin tattaunawa kan yadda juyin mulki ke ta’azzara a yammacin Afirka, wanda tun a 2020 aka yi ta samun juyin mulkin da ya dora sojoji kan karagar mulki a kasashen Mali, Burkina Faso, Guinea da Nijar.
A watan Nuwamba, an samu wani yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a kasar Saliyo, sai dai ya yi sanadin mutuwar mutane 21.