• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Ta Samu Kwarin Gwiwar Zuwa Kofin Duniya

by Abba Ibrahim Wada
3 weeks ago
Nijeriya

A hankali dai tawagar ‘yanwasan kwallon kafa ta kasa Super Eagles tana sake samun kwarin gwiwar damar zuwa gasar cin kofin duniya sakamakon hukunce-hukuncen da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA take yi a kan wasu kasashen da suka aikata laifi a lokacin buga wasannin neman cancantar shiga gasar.

Kwamitin ladabtarwa na hukumar kwallon kafa FIFA ya sanar matakin da ta dauka a kan tawagar kwallon Afirka ta Kudu, inda ta rage mata maki uku, sannan ta ci ta tarar kudi.

  • Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
  • Fim Na Nezha 2 Na Kasar Sin Ya Kara Samun Lambar Yabo

Kwamitin ya gano kasar ta yi laifi ne wajen amfani da danwasan da bai kamata ya buga wasan ba, wanda tawagar da fafata da kasar Lesotho wato Teboho Mokoena da aka buga a ranar 21 ga watan Maris na shekarar 2025.

FIFA ta ce amfani da danwasan ya saba da sashe na 19 da kundin laifuka na hukumar, sannan ya kuma saba da sashe na 14 na kundin shirye-shiryen farko-farko na gasar cin kofin duniya na shekarar 2026.

FIFA ta ce bayan nazarin binciken da aka gudanar, ta kwace nasarar da Afirka ta Kudu ta samu, sannan ta ba kasar Lesotho nasara a wasan. Wadanda aka ladabtar saboda laifukan dai suna da kwana 10 domin daukaka kara a gaban kwamitin daukaka kara na kwamitin ladabtarwa na Hukumar FIFA.

LABARAI MASU NASABA

An Sake Saka Sunan Osimhen A Cikin ‘Yan Takarar Kyautar Gwarzon Dan Wasan CAF Na Bana

Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars

 

Me Hakan Ke Nufi Ga Tawagar Nijeriya?

Ga Yadda Tsayuwar Rukunin C Yake

A ranar 9 ga watan Satumba ne tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta tashi da kunnen doki a wasan da ta buga da tawagar ta Afirka ta Kudu a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya. Bayan wasan ne kasar Afirka ta Kudu ta kara zama a saman teburi da maki 17 cikin wasa takwas da ta buga a Rukunin C.

Tawagar Jamhuriyar Benin ke biye mata da maki 14, sai kuma Nijeriya da ke mataki na 3 da maki 11.

Sai dai kuma Nijeriya ta kasance tana da maki daya ne da na Rwanda da ke mataki na 4, sai kuma kasar Lesotho da ke da maki 6 a mataki na 5, sai kuma Zimbabwe ta karshe da maki 4.

Kasashe tara ko 10 ne za su wakilci nahiyar Afirka a gasar cin kofin duniya na 2026, wadda kasashe 48 za su fafata kuma kasashen Amurka da Medico da Canada za su karbi bakunci.

 

Canjin Da aka samu Bayan Hukunci

A ka’idar wasannin neman gurbin, duk tawagar da ta kare a mataki na daya daga kowane rukuni guda tara na nahiyar Afirka ce za ta samu gurbi kai-tsaye. Daga baya sai a zabo hudu mafiya kokari da suka kare a mataki na 2, inda za a fitar da daya daga cikinsu sannan ta kara da wata tawagar daga nahiyar.

Yanzu da aka rage wa Afirka ta Kudu maki uku, zai zama tana da maki 14 kenan, dai-dai da tawagar kasar Benin, ita kuma kasar Lesotho ta samu karin maki uku zuwa maki tara maimakon shida a baya kafin a kara mata maki uku.

Yanzu wasa biyu ne suka rage wa kowace tawaga, inda Nijeriya take bukatar samun nasara a wasannin guda biyu. Idan ta samu nasara a wasannin da za ta buga da Lesotho da Benin, zai zama Nijeriya da maki 17 ke nan jimilla.

Sai dai kuma hakan zai ta’allaka ne da wasannin sauran kungiyoyin, domin idan Afirka ta Kudu ko Benin daya daga ciki ta ci wasa daya, ta yi canjaras a wasa daya, za ta koma maki 18. Amma idan ta yi rashin nasara a wasa daya, ta ci daya za ta tsaya da maki 17 ne, daidai ke nan da idan Nijeriya ta samu nasara a wasanninta biyu na gaba.

Ita Benin yanzu damarta ta karu, kuma akwai wasa tsakanin Nijeriya da Benin, wasan da za a iya kira da raba gardama domin shi ne wasan Nijeriya na karshe a rukunin na C.

Ke nan Nijeriya ta fi bukatar samun nasara a wasanninta biyu na gaba, sannan Afirka ta Kudu da Benin su rasa wasanninsu biyu na gaba, inda za ta kara da maki 17, su kuma suna 14. Haka kuma idan Nijeriya da Afirka ta Kudu suka karkare da maki daya, Super Eagles na bukatar kwallaye fiye da Afirka ta Kudu haka ita ma Benin. Yanzu haka Afirka ta Kudu na da yawan kwallaye +8, yayin da Nijeriya ke da +2.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sake Saka Sunan Osimhen A Cikin ‘Yan Takarar Kyautar Gwarzon Dan Wasan CAF Na Bana
Wasanni

An Sake Saka Sunan Osimhen A Cikin ‘Yan Takarar Kyautar Gwarzon Dan Wasan CAF Na Bana

October 22, 2025
Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars
Wasanni

Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars

October 22, 2025
Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta
Labarai

Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta

October 20, 2025
Next Post
Jami’in MDD: Shawarar GGI Za Ta Jagoranci Duniya Zuwa Samun Kyakkyawar Makoma Mai Cike Da Adalci

Jami’in MDD: Shawarar GGI Za Ta Jagoranci Duniya Zuwa Samun Kyakkyawar Makoma Mai Cike Da Adalci

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

October 25, 2025
Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa

October 25, 2025
Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi

October 25, 2025
Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Thomas Etuh: Gwarzon Ɗan Kasuwa Na 2025

October 25, 2025
Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.